A cewar rahoton Ofishin Yada Labaran Hauza, yayin babban taron kasa da kasa karo na 21 kan "Ka'idar Mahdawiyya" wanda aka gudanar a Masallacin Jamkaran Ayatullah Alireza A'arafi, Shugaban Makarantun Hauza na kasa, yayin da yake jaddada bukatar komawa ga Mahdawiyya ta gaskiya da kuma Intizar mai aiki, ya bayyana cewa: "Duniyar Musulmi a yau fiye da kowane lokaci tana buƙatar 'Mahdawiyyar Muƙawama' da kuma 'Intizar mai ci gaba'."
Ya bayyana cewa ya kamata Intizar a lokaci guda ya samu jan hankali na duniya don jawo hankulan zukatan masu sha'awa, kuma a lokaci guda ya samar da abin da zai sa a kauce wa da kuma yin muƙawama ga tsare-tsaren ma'abota girman kai da 'yan Sahyoniya.
Gargaɗi Game Da Karkatattun Fassarorin Karshen Zamani
Ayatullah A'arafi, yayin da yake ishara da karkatattun cibiyoyi uku na tunani, wato "Yahudanci na Sahyoniyanci," "Kiristanci na Sahyoniyanci," da kuma "Fassarar Yancin Duniya ta yammacin Turai," ya yi gargaɗi cewa wadannan cibiyoyin a aikace suna hade da juna kuma suna goyon bayan mulkin mallaka, wariyar launin fata, da kuma goyon bayan mulkin Sahyoniyanci.
Ayukan Asali Guda Uku Wajen Yada Mahdawiyya
Ya lissafo ayukan asali na ra'ayin Mahdawiyya kamar haka:
1. Gabatar da ra'ayin Mahdawiyya cikakke kuma na hankali ga duniya mai jin kishirwar ceto.
2. Suka ta ilimi da kuma nazarin tushen karkatattun ra'ayoyin imani da mai ceto.
3. Kasancewa da aiki a fagen aiki, saboda wadannan ra'ayoyin na banza sun zama makaman mulkin mallaka.
Intizar Ba Tare Da Muƙawama Ba, Nakasasshen Intizar
Shugaban Makarantun Hauza, yayin da yake jaddada muhimmiyar rawar gwagwarmaya (muƙawama), ya bayyana cewa: "'Intizar ba tare da gwagwarmaya ba, ragon Intizar ne,' kuma duniyar Musulmi tana bukatar Intizar irin wanda zai hada kan al'umma kuma ya basu damar tsayawa a gaban shirye-shiryen zalunci na maƙiya."
Kira Ga Hadin Kan Duniyar Musulmi
Ayatullah A'arafi, yayin da yake ishara da mummunan hari daga cibiyoyin ma'abota girman kai, ya yi gargaɗi cewa idan al'ummar Musulmi ba su haɗa kai ba tare da dukkan mazahabobi da kabilunsu, za a kai musu hari daya bayan daya. A cewar sa, makiyi ba ya son komai face wulakanci da bautar kai ga Musulmi, kuma har ma suna amfani da kafofin addini da na ilimi don cimma manufofinsu.
Sakon Karshe Na Babban Taron
Ayatullah A'arafi a karshe, ya bayyana cewa sakon babban taron shi ne "'Komawa ga Mahdawiyya ta gaskiya da kuma Intizar na gaskiya,' wanda shi ne wanda ke samar da wayewa da kuma kare bil'adama, sannan kuma yana da matsayi mai tsauri a gaban masu girman kai da 'yan Sahayuniya." Ya jaddada nauyin da ya rataya a wuyan malamai da kwararru kan daukar nauyin bayyanawa da kuma yada wannan ra'ayi a duniya.
Your Comment